MAƊACIYAR ZUMA
“Aaah! Mutuwa? Asma’u me nake ji haka?”
Na ƙwalla ƙara mai ƙarfin gaske
daga banɗaki inda nake wanka tare da jefar da littafin dake hannuna ga ruwa na malala daga cikin bahon wanka a
yayin da na yunƙura da ƙarfi dan fita waje na
tabbatar da abin da yake faruwa. Na garzayo da gudu a ɗimauce don zuwa falo, saura ƙiris na
sha kwana kenan da zata sada ni da ɗakin sai naga hoton surar jikina tsirara
lulluɓe da kumfa a jikin gilashin ƙofa, wanda hakan yasa na lura cewa ashe babu
kaya a jikina. Sai na koma na ɗauraye kumfar dake jikina sannan na sanya kayana
na fito.
Ya zamar min al’ada duk
safiyar lahadi, inda nake shiga bahon wanka wato (jacuzy) don
yin wanka. Tunda yake ƙarshen mako ne, sai nayi amfani da wannan damar inda nake
karanta littafi kafin na fita don
halartar daurikan aure. Lahadi ta zamo ranar da aka fi yin ɗaure-ɗauren aure a
garin Kano. Dan haka yasa ta zama tamkar ranar sakewa ga mutane da dama saboda
damar da take basu na hutawa ba tare da sun fita wajen harkokinsu ba tun sassafe kamar
yadda aka saba.
“Yanzinnan naji a rediyo,”
Asma’u ta cigaba da faɗa min, “yanzu naji Nasir Zango yana faɗa a shirinsa na Inda Ranka.” Asma’u ta kasance ma’abuciyar jin rediyo. Kullun safiya tana tashi ta kamo
Muryar Amruka, BBC Hausa, DW ko RFI Hausa don ta ji labarai kafin daga bisani
ta murɗo rediyo Freedom dan ta saurari shirin Inda Ranka na karshen mako
wanda jajirtaccan ɗan jaridar nan yake gabatarwa.
“Kina nufin ya mutu?” Na
tambayeta dan na samu tabbaci.
“Ya mutu da gaske.” Asma’u
ta tabbatar min.
“To amma ya akai kika
tabbatar shi ne?”
“Kwatancensa da na ji an faɗa.
Askinsa, kayansa da kuma yanayin fuskarsa.” Asma’u ta ci gaba da yi min jawabi,
“iri ɗaya da kwatancen da muka bayar lokacin da muka kwana uku bamu ganshi ba.”
Mun shiga wani zamani wanda
akayi yayin zuwa ƙasashen waje, musamman ƙasar Malaysiya inda iyaye suke tura ‘ƴaƴansu don yin karatu. Kowa ba shi da wani buri sama da yaga ya fitar da ɗansa
ƙasar waje musamman idan yaro ko yarinya ya sami labaring tafiyar aboikinsa ko
ƙawarta. Suna tafiya da niyyar yin karautun
kamar yadda suka sanar da iyayensu tun da fari. Amma da zarar sun je ƙasar sai
su rikiɗa su zama kamar ‘yan yawon buɗe ido da shaƙatawa, sune kalle-kalle da
halartar gidajen rawa, da gidajen shaye-shaye da sauran gidajen shagala. Kai a
ƙarshe ma sune suke zama gawurtattun masu ta’ammali da sha da safarar miyagun ƙwayoyi
wanda suke zama kamar wata annoba ga muhukuntar ƙasar. Amma saboda kuɗin shiga
da suke samarwa da ƙasar, sai muhukunta sukayi shiru da bakinsu ba tare da ɗaukar
wani mataki ba. Sai wanda da ya taɓa zuwa ƙasar ne kawai zai bada labarin haƙiƙanin
miyagun ayyukan da yaran suke tafkawa a can.
Ni dai na kasance mashahurin
ɗan kasuwa mai zuwa ƙasashen duniya daban-daban don na sayo haja ko na sayar. A
bisa haka ne zan bada wani labari da ya
faru a kaina. Wata rana ina balaguro zuwa ƙasar Dubai dan harkar kasuwanci na,
sai na shiga jirgi tare da wani saurayi wanda ke kan hanyarsa ta komawa
Malaysia inda yake karatu. Muka zauna a waje ɗaya a ɓangaren babbar kujera,
wato dai sahun masu hannu da shuni wanda a turance ake kira da Fisrt Class.
“Yaro kai ɗan Najeriyane?”
Nayi wuf na tambayeshi cikin harshen turanci.
“E,” shi ma ya amsa min.
Na yi masa magana ne don mu ɗan
yi taɗi tun bayan da na lura cewa duk munyi jugun-jugun kamar a gidan mutuwa.
Nan ta ke na canja harshe zuwa harshen Hausa lokacin da na fahimci cewa shi ma
saurayin bahaushe ne kamar ni. Ganin cewa ya sami ɗan uwa kuma abokin hira, sai
yaron yaji daɗi sosai. Nan fa hirar mu tai nisa sosai kuma ta ɗau shauƙi inda
nake tambayarsa shi kuma yana bani amsa. Saboda tsabar nishaɗin hirar har sai
da na manta cewa a jirgi nake tafiya, na manta da doguwar tafiyar dake gabana,
har ta kai sai da na manta da yinwar da nake ji kafin naci abincin da jami’an
jirgin suka kawo min. Shi kansa abincin ban samu damar wai-wayarsa ba har sai
da na samu wani ɗan taƙi inda hirar mu ta tsagaita. Yayin da na tambayeshi ko
waye mahaifinsa, sai bayanan da na samu suka tabbatar min da cewa ya fito daga
gidan wani Minista wanda ludayinsa ke kan dawo a gwamnati mai ci ta wannan
lokacin. Ganin cewa a lokacin da yaje Najeriya ba lokacin hutu bane, sai na sa
ke tambayarsa ko me yaje yi Najeriya. Nan ma sai ya sake gayamin cewa ya je ne
don ya halarci bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yar uwarsa (Birthday Party)
wadda ita ma take karatu a ƙasar Amruka. Jin haka yasa na tuna da wani lokaci a
baya wanda yawan ziyarar da ɗaliban najeriya masu karatu a waje ke kawowa gida
yasa na tambayi Hajiya mahiafiyar Haladu, ɗan
yayana wanda tuni ya rigamu gidan gaskiya. Bisa yawan zirga-zirga da
yake yi tsakanin Malaysia da Najeriya yasa na tambayi mahaifiyarsa cewa,
“Hajiya shin wai ina ne haƙiƙanin inda
yaronnan yake karatune. A nan yake yi ne ko kuma a waje saboda ina ganinsa a
gida kusan ko wace rana.” Na tambayeta cike da mamaki.
Yayin da na tambayi abokin
tafiyata, wato ‘yan samari, shin ko me suke yi idan suka zo Najeriya. Nan ma fa
sai ya bani amsa da cewa ai suna zuwa shan fura ne kawai da kuma cin tsire a
wani kantin sayarda kayan ƙwalam-da-maƙulashe da ke kan titin zuwa Zaria.
“To amma ya kuke fama da
zirga-zirga, kullun kuna kan hanya daga Malaysia zuwa Najeriya?” Na tambayeshi
cike da mamaki da ta’ajibi.
“Ya wancinmu anan iyayenmu
ne suke saya mana jirgin yawo don biyan buƙatunmu ta yadda da munji kewar gida
muna da damar mukai ziyara a kowane lokaci don mu sada zumunci ga ‘yan uwa da
abokan arzuƙa.” Ya amsa cikin annashuwa da alfahari.
“To amma ya akayi naga kuma
ka hawo jirgin haya?”
Sai ya amsa da cewa, “ nawa jirgin ne ya lalace. Amma mahifina
ya rigaya ya biyamin kuɗin tikiti da zan yi amfani da shi har tsawon lokacin da zan gama karatuna.” Ya
zira hannu a cikin jakarsa don ya fito min da takardun da za su gasgata abin da
ya faɗa min. Ko da ya zaro takardun sai ga bandir ɗin Dalar Amruka ta faɗo daga
cikin jakar wanda ganin haka yasa naji ba ni da wata buƙata ta ganin takardun. Ganin irin fantamawar da yakeyi sai na
tmbayeshi don ya gayamin ko wace makaranta yake zuwa a Malaysia. Sunan
makarantar da ya faɗamin sai naji yayi dai-dai da sunan makarantar da ɗan
yayana, Haladu yake halarta. Jin haka sai yasa na tambayeshi:
“Ko ka san Haladu?” wanda shi ne sunan ɗan yayan nawa da
yake karatu a Malaysia. Ya ɗan rufe idanunsa kadan cikin tunani da rikici dan
ya gano mutumin da nake kwatanta masa.
“Khalid Usman,” sai na ƙara masa haske dan ya gane wanda
nake kwatanta masa cikin sauki.
“Oho...” sai ya kece da dariya, “kana nufin Ɗan Hajiya
ko? Ai idan ba kace Wizzy ba to ba zan taɓa ganewa ba.”
Bayan mun isa zuwa ƙasar Malaysia sai na ga ya dace na ɗan
tsahirta a ƙasar zuwa na ‘yan wasu
kwanaki don na ɗan kewaya ko naga wata haja da zan iya siya kafin na wuce zuwa
Dubai. Bayan mun fito daga ɗakin
bincike, sai nayi masa tayi ko zai kwana a masauki na kafin safiya, amma sai yace
a’a. Daga nan sai mukayi musayar adireshi inda yayi alkawarin cewa zai zo ya ɗaukene
washegari daga masauki na don nakai ziyara makarantarsu. Mukai sallama na shiga
motar haya don zuwa masauki inda na bar yaron tare da jerin gwanon motoci da
suka zo su tarbeshi.
Washegari saurayinnan yazo ya ɗaukeni izuwa makarantar.
Lokacin da na shiga na zata ko ina Najeriyane sakamakon yawan ‘yan Najeriya da
nayi ido huɗu da su. Dukkanninsu suna cikin farin ciki da jin daɗi kuma kowa
yana yin abin da ya ga dama dan babu mai kwaɓarsu. Babu mai cewa ta tafasa
balle ka sauke. Abin dai ba kyan gani yadda suke cakuɗe-ɗeniya tsakanin maza da
mata har ta kai da ba’a iya ban-bancewa tsakanin jinsi. Suna ta cashewa abinsu,
ga kiɗa na tashi ta ko’ina daga cikin motocin dake ajiye a wurin. Kayan maye a
wurin sun zama kamar ruwan sha kowa sai kwankwaɗa yake. Wasu na tayiwa kansu
allurai, wasu kuma nata busa hayaƙin taba sama, yayinda wasu ke shaƙa hodar
iblis cikin hancinsu. Ina tsaye sai ga
wasu yara mace da namiji sunzo wucewa suna tafiya suna tunɓele da karafkiya
suna haɗa hanya kamar ‘ƴa’ƴan agwagwa. Na kiɗima ƙwarai da gaske yadda naga
yarinyar tana haɗiyar ƙwayoyi tana binsu da ruwan magani, (syrup). Ganin yadda
aka san matan Hausawa da tarbiya, sai na yunƙura don naje wajen yarinyar nayi
mata magana nace ‘‘ƴan mata ko ke ba
bahaushiya bace,’ sai kawai naji tayi
magana da yaran kuma a cikin kammalalliyar Hausa kamar jakar Kano. Bayan sun
matso kusa da inda nake tsaye sai naga ashe Salima ce ‘ƴar abokina wanda ya taɓa
yin gwamna a maƙwabciyar jahar mu. Shi kuma yaron da ke tare da ita ko da na
tambaya ko shi waye sai aka gaya min cewa ɗa ne ga wani babban Jami’in gwamnati
daga Jahar Enugu wanda ya taɓa rike muƙamin Ministan Man Fetur a gwamnatin da
ta shuɗe.
Ɗan Hajiya da abokansa suna ɗaki bayan sun gama buguwa da
kayan maye, suna tattauna yadda zasu halarci wani casu da za’ayi daddare.
“Wizzy wai
ya za’ayine kasan fa akwai casu yau da daddare?” Abokin Ɗan Hajiya mai suna
Zicko ya tambayi abokinsa. Asalin sunansa shi ne Adamu amma ganin cewa sunan
yayi masa nauyi sai ya canja zuwa Zicko don ya tafi da yanayinsa.
“Ai yau akwai wani babban casu, duk wani yaro mai ji da
kansa a ƙasar nan zai je.” Khalid Ɗan Hajiya ya faɗa.
“Dole ne fa mu cinye kowa a wajen casunnan kai ka sani
abokina.” Ɗayan abokin nasu mai suna Bross shi ma ya tofa albarkacin bakinsa.
Yana magana ga kuma naɗin tabar wiy-wiy a hannunsa yana ta faman zuƙa yana busa
hayaƙin sama ta hanci da baki kamar
tsohuwar motar da salansarta ta fashe. “Akwai ragowar ƙwayoyi kuwa? Kun
san fa da ita ne zamu iya wuce sa’a a ko’ina. Yawan ƙwayar da muka sha shi zai
sa mu burge kowa da kowa a wajen.”
“Ka gama har wasu ma bawa waɗanda basu da ita da yawa.”
Zicko ya jaddada abinda abokinsa Bross ya faɗa.
“Duk ƙwayoyinnan fa
sun ƙare. Na shanyesu duka yau da safannan kuma kun san kwanannan kuɗi wahala
suke.” Ɗan Hajiya ya maida musu da amsa.
“Haba mutumina, meye amfanin Hajiya idan ba zata baka kuɗi
ba? Kawai ka gaya mata baka da kuɗi za ta sa wannan ƙanin babannan naka ya ba
ka.”
Tsaowon
lokaci ke nan bayan
dawowata daga ƙasar Malysia inda naga irin masha’a da yaranmu ke tafkawa da sunan karatu. Wata rana Ɗan Hajiya ya dawo gida
ya gayawa mahiafitayrsa ƙaryar cewa anyi hutun makaranta kamar yadda ya saba
duk lokacin da yake so ya zauna a gida. Ina zaune a gida tare da matata Asma’u ina gaya mata abinda yake damuna an halayyar Ɗan Hajiya.
“Wannan sha-shan yaron,” na kama faɗa cikin
fushi. “ya ƙi ya nutsu ya san
abinda yake ciki. Yaƙi ya maida kai akan karatunsa gashi kuma kasuwarma yaƙi ya
fuskanci abinda ake koya masa. Ni dai ban san yaushe zaiyi hankaliba.”
“Alhaji,” Asma’u ta fara bani haƙuri, “kayi haƙuri kasan yaran yanzu
sai da haƙuri da kuma addu’a. Kullun ina gaya maka
ka daina sa kanka cikin damuwa idan kuma ba haka ba sai hawan jini ya kamaka.”
“Amma dai ai ba’a zuba ido ba a bar
abubuwa su ringa faruwa sasakai ba. Matasannan fa sune manyan gobe kuma a
wannan lokacin ne ya kamata su ginawa kansu makoma me kyau. Amma ki duba ki
gani ba abinda suke shagala da shi sai shaye-shaye, sata da zuwa gidan rawa.
Yanzu kinga ma fa ya sayarda motar da Hajiya ta saya masa yayi mata ƙaryar cewa
wai an sace.”
Bayan na gama banbaimi na ban zame ko ina ba sai gidan
Hajiya don na gaya mata abinda yake faruwa. Duk da yake ƙarfe 3:00 na yamma ta
riga ta yi lokacin da na iske gidan,
amma har kawo wannan lokacin Ɗan Hajiya bai tashi daga barci ba saboda kayen
mayen da yasha daren jiya.
“Hajiya na gaya miki kina shagwaɓa yarannan. Abin yayi yawa Hajiya, ace
yarannan ya zama kamar ma shi ne babar taki sai abnida yace shi kike yi. Yanzu
ga shi yazo ya share waje ya zauna sama da wata uku kuma yana gaya miki cewa
wai anyi musu hutune. Su makarantar basu da hankaline.”Ina ta faɗa cikin fushi ina girgiza kaina cikin nadamar Ɗan Hajiya.
Nan fa Hajiya ta hayayyaƙo ƙaina tana ta balbaleni da
masifa tana cewa, “me yasa zaka takurawa ɗa
na iye? Ka ƙyale shi ya sakata ya wala.”
“Amma Haji...”
“Amma me?” Hajiya ta katseni kafin
na ƙarasa. “Da ma ina so na gayama
cewa wai baka san kayi min laifi ba da ka koroshi daga kasuwa kuma shi ne yanzuma
har kake iya buɗe baki kana gayamin wannan maganar. To gaya min mai yayi ka
koroshi, iye?” Hajiya ta tambayeni
cikin fushi tare da tsare ni da ido tsuru-tsuru, ta tsaya a gabana tana
gallamin harara kamar ta cukumeni da kokawa.
“Na kama shi yana ɗibar kuɗi shi yasa na kore shi. Kuma da ma na gaya masa
kada ya sake na ƙara kamashi yana yin sata.”
“Amma ka san cewa kuɗin ba naka bane kai kaɗai ko?” Ta faɗa a cikin gatse. “To shi ma yana da gado.”
“Amma dai Hajiya a matsayina na ɗan uwan mahifinsa bai kamata ina gani ba
yarannan ya lalace. Ai al’umma sai su tsine min
suce ban sauke haƙƙin da ya rataya a wuyanaba.” Na cigaba da yi mata jawabi la’alla ta fahimce ni.
Bayan tafiyata a wannan rana, ashe Ɗan Hajiya da abokansa
suna da casu da daddare wanda suke kira shakwaro (shokorology). Ɗan hajiya yaje
wajen mahifiyarsa ya gaya mata ƙarya da gaskiya kamar yadda ya saba duk lokacin
da yake buƙatar wani abu a hannunta. Ita kuwa sai ta ba shi kuɗi wanda da su ne
yake biyan buƙatunsa na siyan kayan maye. Bayan da dare yayi Ɗan Hajiya da
abokansa suka yi shiga irin wadda suka saba yi, tsukakken wando da
matsatstsiyar riga ga ɗamara wato belt
a waje ga rabin ɗuwawunsu shi ma duk a waje ana gani, wato sukayi shiga irin ta
samfurin suwaga. Ba iya nan suka tsayaba, kai hatta askin kansu ma irin
samfurin nanne mai taken Bollatalli. Bayan sun sha ƙwaya tun a gida ta fara yi
musu karo sai suka fita abinsu zuwa wajen casu suna ta tunɓele a hanya. Duk
wanda ya gansu sai ya kauce ya basu waje dan gudun kada su jefashi cikin lambatu
saboda karafniya da suke suna haɗa hanya. Da zuwa wajen casun, sai dukkaninsu saku
zube ƙasa cikin maye saboda basa cikin hayyacin da zasu iya zama ballantana su
tsaya su kalli ma me yake gudana. Gida ya cika da samari maza da mata ana ta
tiƙar rawa.
Can daga tsallaken inda suke rawa wani mutum ya garzaya
zuwa ofishin ‘yan sanda dan bada
rahoton ɓatar motarsa da aka sace bayan
da ya shiga wani kanti dan yayi siyayya akan hanyarsa ta komawa gida daga wajen
aiki. Ya shiga ofishin ‘ƴan sanda a ɗimauce yana
kuka wi-wi hannuwa a ka. Babban jami’in ‘ƴan sanda wato DPO ya
tura mutanensa dan su bi sawun ɓararyin.
Amma sakamakon cewa ɓarayin basu da wata tartibiyar siffa da za’a iya ganesu, sai DPO yace de yaransa su kamo duk wanda suke ganin yayi
shige da masu aikata laifi idan yaso a gane mai laifi da maras laifi daga baya bayan
anyi bincike. ‘Ƴan sanda na fita basu
zame ko ina ba sai inda ake casu da shaye-shaye wajen da nanne masu laifi su
kan samu mafaka. Da isarsu sai kowa ya
gudu abinsa, wasu suka haure ta katanga, wasu kuma suka zillewa ‘ƴan sandan, kai wasu ma sai da akai kokawa da su aka kai ruwa rana sannan
suka samu suka kufce da ƙyar, irin abinnan da Huasawa suke cewa wai da ƙyar na
sha... Amma su kam su gogannaka basu ma san me ake cikiba domin kuwa a sa’ilin ne ma ƙwaya ta fara aiki gadan-gadan. Suna nan kwance sun kasa ko
motsawa balle su gudu inda suke ta barci sharkaf kamar kasa.
“Waɗannan ne ɓarayin." Ɗaya daga cikin jami’an tsaron ya faɗi haka. “Sajen kalle su fa, kalli
kayansu, kalli askinsu, kalli fuskarsu da idanunsu, ai kawai yallaɓai su ne ma.” Nan ta ke ‘ƴan sanda sukayi awan
gaba da su zuwa chaji ofis dan gudanar da bincike inda nanne Ɗan Hajiya ya mace
sakamakon ciwon kansar hunhu da ya tayar masa ba tare da ya sha magani ba bayan
kwana uku muna ta faman nemansa. Ta haka ne mukayi ta nemansa kafin mu ji
labarin bal’in da ya same shi a
rediyo. A washegarine mukaje don ɗauko ragowar gawarsa a ofishin ‘ƴan sanda inda gawar har ta fara ɗoyi sa’anna muka binne shi. Da fatan Allah ya jiƙansa!
No comments:
Post a Comment