Translate

Monday, 13 January 2014

Baya da ƙura



Baya da ƙura


Abubakar Sulaiman Muhd

Tana zaune ta yi tagumi jigum, ga takaici da baƙin cikin duniyannnan duk ya addabeta, ya yi mata katutu ya tsaya mata a rai. Wulaƙanci da tsangwama ba irin wanda bata gani ba a rayuwarta ta duniya. Mai gidanta, Alhaji Maikuɗi ba irin ƙaunar da bai nuna mata ba. Yana santa matuƙa gaya ta yadda ba ya san ganin ɓacin ranta dai-dai da misƙala zarratun. Yadda ya tsani mutuwarsa haka ya tsani ya ganta cikin ɓacin rai da damuwa. Saboda muzgunawar da take fuskanta daga ragowar matan gida, tasa Alhaji ya  yake biya mata hajji da umara duk shekara sannan ya zarce da ita zuwa sauran ƙasashe don yawon buɗe ido duk don ya tausashi zuciyarta.
Alhaji Maikuɗi ya shiga damuwa ƙwarai da gaske ganin yadda uwar gidansa wato Binta ta shiga mummunan yanayi na damuwa da ɓacin rai da baƙin ciki da yawan tunani. Yawan tunani yasa duk ta rame ta bushe ta ƙanjame kamar ragowar yaƙi. Idanun ta duk sun kukkukkunbura luhu-luhu, sunyi ja saboda yawan kuka sakamakon ɓacin ran baƙaƙen maganganun da ake yada mata wanda suke mata turnuƙu a zuciyarta.
Hajiya Binta, Alhaji Maikuɗi yayi mata magana cikin tattausan lafazi mai cike da tausayi. Ki daina wannan yawan kukan da tunani da kike yi.  Wace iriyar baiwace Allah bai miki ba. Baya ga kyan sura da Allah yayi miki ya kuma niimataki da hankali da tunani. Bugu da ƙari, Allah bai barki haka ba  sai ya auraki ga mtum irina inda zaki ji daɗi ki huta. Baki da wata matsala saboda duk abinda kika nema kina samu. Wace iriyar dukiyace ko wane irin jin daɗine bakya samu anan gidan? Dan Allah ina so ki daina wannan yawan kukan. Ki barwa Allah komai, ke ma idan kina da rabo sai Allah ya baki ɗa.
Hajiya Binta ta yi aure tare da mai gidanta Alhaji Maikuɗi kimanin shekara talatin da biyar da suka gabata. Amma tsawon wannan lokaci bata taɓa samun haihuwaba. Ganin cewa Allah ya baiwa mai gidanta tarin dukiya, sai Allah ya sa masa ƙaunar samun wanda zai gaje shi kuma wanda zai ringa yi masa addua ko bayan ba ransa. Duk da matsin lamba da Alhaji yake fuskanta daga wajen danginsa, amma bai taɓa ɗaukar abinda suke faɗa masa yayi aiki da shi kai tsayi ba, ba tare da yin shawara da Hajiya Binta ba. Hakan yasa suke ganin kamar ma ko ta shanye shi ne. Kowa a dangin mijinta ya ɗau karan tsana ya ɗora mata saboda rashin haihuwa. Abubuwa sukai ta taazzara, dangantaka tai tsami tsakaninta da surukanta. Idan ta kawo musu abinci sai suki karɓa, idan ta gaishesu sai su ƙi amsawa, sannan kuma yawan tsangwama ya hana ta halartar duk wani irin taro a dangin, kamar suna, shan zabaina ko wuni. Kai hatta wajen kamu ko buɗar kai sai da ya gagareta zuwa. Dalilinsu na wareta daga cikinsu shi ne kada cuɗanya da ita yasa ƴaƴansu su shafi matsalar rashin haihuwa irin tata. Sai dai kash! sun manta cewa Hajiya Binat ba juya bace domin tsawon shekarun da tayi da mijinta basu tashi a banzaba. Ta sami ciki sau goma sha tara illa dai kawai tanayin ɓarine. Da ba dan hakaba da tuni itama tana nan tare da ƴaƴanta kamar kowa. Da tuni itama ta aurar kamar yadda ragowar ƙawayenta suka aurar. Da tuni itama tana nan da babban ɗanta wanda da yana raye, da ya sami gatan duniyannan daga mahifinsa. Wata biyu da aurensu ta sami juna biyu, mai gidanta kuma yayi mata alƙawarin gida a Abuja da kano inda suke zaune. Sannan yayi mata alƙawarin cewa zai mallaka mata kamfaninsa inda ake sarrafa masa kayayyaki ita da jaririn da zata haifa masa. Amma hakan bai faruba domin duk lokacin da ta sami ciki sai tayi ɓari. Duk waɗannan abubuwa na kyautatawa da kaɓakin arziƙi bata same su ba,  sai dai tana gani suka koma wajen kishiyoyinta waɗanda suka zo bayan-bayanta amma suka haifawa Alhaji magada.
Rannan Hajiya Binta tana zaune a ɗaki ita kaɗai sai ta ɗauko rediyo dan ta saurari wani shiri mai suna Hankalinka Gatanka  daga gidan rediyo Gyara Kayanka inda ake gayyato masana daga fannonin rayuwa daban-daban inda sukeyin bayani kan alamura da suka shafi jamaa. Shi wanna shiri yana maida hankaline wajen tattauna matsalolin da suka fi addabar alumma kuma sukai ƙamari a cikin zamantakewa. Hajiya Binta ta yi baƙuwa jiya, wadda ɗaya ce daga cikin ƙawayenta tun na ƙuruciya wadda ta kawo mata ziyara. A lokacin ziyarar tatane suka tattauna matsalolin da suka dami Hajiya Binta. Sai ƙawar tata ta bata shawara akan ta ringa saurarar wannan shiri wataƙila ta gano menene matsalarta tunda babban baƙon da zaa yi hira da shi a wannan satin likita ne. Ai ko ta namma ta iya jin musabbabin abin da ya jawo mata matsalar rashin haihuwa.
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin na Hankalinka Gatanaka wanda ya saba zuwar muku daga nan gidan rediyo Gyara Kayanka tare da ni Aishatu Sulaiman. Hajiya Binta ta ƙara gyara zama ta ƙara murɗo sautin rediyonta. A tare da ni a cikin shirin na yau muna tare da Dakta Yushau Garba babban likitan jamaa da kare cututtuka na sashen haihuwa da cututtukan mata wato Abstetrics and Gynocology, na babban asibitin ƙwararru na cikin gari. Yau a cikin shrin na yau zamu tattauna da liktane akan matsaloli da illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma yin allurai barkatai ga lafiyar ƴaƴa mata,  musamman ta fuskar hana su ɗaukar ciki da kuma wani lokacin samun haihuwa. Hajiya ta ƙara zama sosai don taji zaa sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi.
Likita a madadin masu sauraro filin Hankalinka Gatanka na yi maka barka da zuwa.Mai sanarwa tayi masa maraba.
Jamaa salamu alaikum. Shi ma yayi musu sallama.
To kamar yadda na faɗa zamu tattauna da likita tsawon saa ɗaya, inda daga bisani zamu baku layukan waya da za ku samemu kai tsaye dan kuyi tambaya ta hanayar bugo waya ko turo rubutaccen saƙo. Layukan da zaa iya samunmu su ne: 0706...80...77,ƴar jaridar ta fadi lambar kuma ta shiga cikin shirin gadan-gadan.
Likita wai shin meye illar da shaye-shayen ƙwayoyi da yin alluarai barkatai ke jawowa ga ƴaƴa mata musamman ɓangaren samun ciki da kuma haihuwa? Ƴar jaridar ta tambaya.
To da farko dai zan fara da tambayarki ta farko wato illar shaye-shaye ga ƴaƴa mata ta fuskar samun ciki da kuma haihuwa. Da farko dai abinda ake nufi da ƙwaya shi ne dukkan wani abu da zaa iya amfani da shi don a sha, ko a haɗiya, ko a shaƙa, kuma dalilin haka ya jawo sauyin yanayi a jiki ta hanyar samar da kuzari, ko kasala, ko samarda canjin tunani da juyawar hankali ko ƙwaƙwalwa.
To abinda ake nufi da shan ƙwaya shi ne amfani da ƙwayoyin da a likintance basu zama dole ba, ko a sha ba tare da umarnin likitaba , ko a sha fiye da ƙima ko kuma shan ƙwayoyin da doka ta haramta. A taƙaice dai akan iya cewa abin da ake nufi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi shi ne yin amfani da magani dan wani dalili saɓanin aikinsa na asali. Ko kuma yin amfani da haramtattun magunguna ko wanda ya saɓa da alada ko zamantakewa.
To illar shaye-shaye ga mata yana da haɗarin gaske saboda yakan iya hana su haifar yaro a raye abin da aka sani da ɓarin ciki. Shi ɓarin ciki yana faruwane lokacin da ɗan tayi wato festus a turance, ya kai kimanin sati ashirin a mahaifa. A bincike na baya-bayannan an gano cewa kimanin mata  6000 ne sukayi ɓari lokacin haihuwa a wata shidan farko na shekarar da ta gabata wanda dukkaninsu bincike ya tabbatar da cewa suna taammali da miyagun ƙwayoyi. Ana ɗaukar mabiyiya da kuma jini dan ayi gwajin sinadarin nicotine a jikin uwa. Shi wannnan sinadari  yana saka kuzari ko watstsakarwa inda ake samunsa a cikin abubuwa kamar irin su cocaine. Akwai ragowar magunguna kamarsu  amphetamine da sauran magunguna masu rage raɗadi kamar su morphine. Sauran su ne kamar su codein da kuma tabar wi-wi da suransu. Sakamakon binciken ya nuna cewa yawan sinadarin nicotine da yake a cikin jinin matan ya zarta  kaso 19 cikin ɗari yayinda wasu kuma aka gano cewa suna ɗauke da wani adadi mai yawa na sinadarai masu sa kasala wato stimulatns, wanda shi ma dai yana da alaƙa da shaye-shaye ba bisa ƙaida ba. Amma hakan kuma ba yana nufin cewa duk matan da sukeyin ɓariba suna taammali da miyagun ƙwayoyi.
Hajiya Binta na zaune tana sauraron rediyo, bata san lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta ba. Bayanda ta saurari jawabin likita, sai ta ga ashe  itace ta jefa kanta cikin duk irin musifar da ta tsinci kanta a ciki ba. Tana kuka tana cewa, na cuci kaina. Lokacin da ina buduruwa da bayan nayi aure nayi ta shan miyagun ƙwayoyi wai ni ina ganin burgewace. Kaico na, yanzu gashi akan rashin haihuwa ba irin wulaƙancin da ban gani ba. Nan ta share hawayenta ta cigaba da sauraren rediyo yayinda likita ya cigaba da bayani.
To yanzu sai tambayarki ta biyu, wadda tayi magana akan yin allurai ba bisa ƙaida ba. To kamar yadda aka sani itama allura tana da illarta ga lafiyar kowa da kowa, musamman ga ƴaƴa mata a matsyinsu na iyaye. Da farko dai idan akace allura ana nufin wata hanya ta zuba ruwan sinadarin magani ga jiki ta hanyar yin amfani da allura da sirinji tare da  tsira alluarar a cikin jiki gwargwadon  zurfin da ya dace a cikin fata. To a sakamakon yawan matsaloli da allura ke tattare da shi, hukumomin lafiya na duniya suke umarni da a ringa amfani da magani na sha dan kaucewa wadannan matsaloli.
To tunda ya zamana cewa yawancin matasa su suke amfani da alluarai ba bisa ƙaida ba ta jijiyoyin jini wato intravenous don su bugu. To kinga ke nan yawan haɗarurrukan zasu fi afkuwa ga matasa kenan. Yawancin waɗannan allurai sune allurar cocaine , pertozocine da kuma  fortwine, wanda kowacce daga cikinsu tana da illa ga jiki. Haɗarin abun ba wai kawai ya tsaya a bugarwa bane kawai, babbar illar shi ne sinadaran da ke cikin irin waɗannan allurai kan iya sanya mace yin ɓari. Bayan haka kuma suna zama hanyar yaɗa cututtukan jini a tsakanin alumma. Misali ai kinga yaran suna da wani wuri inda suke zuwa akeyi musu allurar, wasu kuma sukan sayi alluran su aje a gidanjensu. To amma duk da haka za ki ga ko waɗanda suka aje alluran a gidajensu, za ki tarar cewa ba su kaɗai ne suke amfani da su ba. Su  kuma masu zuwa kanti dan ayi musu alluarar, nan ma dai za ki tarar cewa akwai jama da yawa waɗanda ke zuwa don ayi musu allurar , kuma mafi yawan lokaci da sirinji guda ɗaya. Tunda shi mai kantin kuɗi kawai yake nema, kenan ko mutum nawa ne kawai zai iya yi musu alluara da sirinji guda ɗaya. Shi dai indai buƙatarsa ta biya, ya amshe ƴan kuɗaɗensa shi ke nan. To tsautsayi idan mai ɗauke da wata cuta irin HIV/AIDs   ko kuma ciwon ƙoda wato Hepatitis B da C a turance yaje akayi masa alluara, sai wani ko wata shi ma yaje akayi masa da wannan sirinjin da akayiwa mai ɗauke da waɗannan cututtuka, to akwai haɗarin kamuwa da cuta. To kuma tunda su masuyin irin waɗannan allurai basu da horo da ƙwarewar likitoci na ainihi, to zaki ga suna yin abin ne ba tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace ba. Sakamakon haka, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa a cikin mutum miliyan 21 da suke kamuwa da ƙwayar cutar HIV/AIDS da kuma ciwon hanta ko Hepatitis C, kimanin mutum 260,00 ne suke kamuwa da cututtukan duk shekara ta sanadiyyar yin amfani da alluarai da sirinjai marasa tsafta, ko yin allura ba bisa ƙaida ba, ko kuma yiwa mutum fiye da ɗaya alluara da sirinji guda ɗaya, ko kuma yin allura ba tare da wanke hannu ba, ko ba tare da ansanya safa ba dan kariya, ko kuma yin amfani da sirinjin da baa rufeba da dai makamantan abubuwa  shigen waɗanda muka lissafa.
A ƙarshe Hajiya za ki ga cewa idan aka haɗa duka, shaye-shayen da kuma alluaran, za ki ga cewa suna da illa ga lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa ta hanyar rage ƙarfin jiki da gurgunta ƙarfin garkuwar jiki abinda aka fi sani a turance da antibody mechanisms, da kuma jawo kansar hunhu, sannan kuma su jawo yawan yin fushi wato depression.
Da jin bayanin da likita yayi sai Hajiya Binta ta fara zargin kanta tare da tabbatarwa da kanta cewa itama tana ɗauke da waɗannan miyagun cututtuka. Nan ta ke ta faɗa kogin tunani inda ta tuna wasu lokuta a baya da take tambayar mijinta zuwa asibiti amma sai ta zagaye ta tafi kantin sayarda magani dan ayi mata allurar maye. Ba komai ya tayar mata da hankaliba sai yadda ta tuna wani lokaci a baya yayinda abin ya ciyota, dole ta tashi ba tare da umarnin mijinta ba ta fita don ayi mata alluara. Ko da ta isa kantin magungunan sai ta tarar da layin mutane maza da mata kowa yana so ayi masa allura. Amma maimakon suyi haƙuri a kawo sababbin sirinjai, sai kawai suka ringa miƙa hannayensu anayi musu allurar da ƙwaya ɗayan sirinjin da ya rage.
Bayan da Alhaji ya dawo gida, sai ya isketa a inda ta gama saurarar rediyo kwance male-male babu kuzari a jikinta kamar gawa. Alhaji ya ɗauketa dan ya kaita asibiti dan ayi gwaji a gano abinda yake damunta. Tun a baya Alhaji yayi ƙoƙarin kaita asibiti amma duk lokacin da ya bujuro mata da maganar sai ta ɓata rai. Shi kuma sai ya ƙyaleta saboda baya san ya ga ɓacin ranta. Da Alhaji ya gaji da irin wannan hali na ta, ga kuma cuta taƙi ci taƙi cinyewa kullun sai rama take tana ƙarewa kamar kuɗin guzuri, dole tasa ya ɗauketa ya kaita asibitin.
Bayan sun fito daga ɗakin gwajine sai sakamakon bincike ya nuna cewa Hajiya Binta na ɗauke da ciwon sida AIDS , da kuma matsanancin ciwon hanta hepatitis C, da ciwon hunhu pulmonary disease  da  anthrax, da kuma ciwon ƙoda renal failure, wanda dukkaninsu suna da alaƙane da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da alluran maye. Bayan sun fito ne sai ta roƙi mai gidan nata da ya rufa mata asiri kada ya bayyanawa ragowar kiyoshinta halin da take ciki, wanda nan take yayi mata alƙawarin hakan.
Ganin cewa ba zai iya zama da mutumin da yake ɗauke da irin waɗannan cututtukaba kashi-kashi dan gudun kada ragowar iyalansa su kamu, sai ya saya mata gida a wata unguwa ta daban sannan ya cigaba da ɗawainiya da ita ta fuskar abinci da magani har zuwa lokacin da ta tunkuyi burji, wata biyu kacal bayan rabuwarsu. Amma duk da haka Alhaji bai furta mata kalmar saki ba saboda tsabar ƙauna da yake mata, don har ta mutu tana nan a matsayin matarsa ta aure inda yake fatan sake haɗuwarsu a aljanna a matsayin mata da miji.

No comments:

Post a Comment