Baya da ƙura
Abubakar
Sulaiman Muhd
Tana zaune ta yi
tagumi jigum, ga takaici da baƙin cikin duniyannnan duk ya addabeta, ya yi mata katutu ya tsaya mata a rai. Wulaƙanci da
tsangwama ba irin wanda bata gani ba a rayuwarta ta duniya. Mai gidanta, Alhaji
Maikuɗi ba irin ƙaunar da bai nuna mata ba. Yana santa matuƙa gaya ta yadda ba
ya san ganin ɓacin ranta dai-dai da misƙala zarratun. Yadda ya tsani mutuwarsa
haka ya tsani ya ganta cikin ɓacin rai da damuwa. Saboda muzgunawar da take
fuskanta daga ragowar matan gida, tasa Alhaji ya yake biya mata hajji da umara duk shekara
sannan ya zarce da ita zuwa sauran ƙasashe don yawon buɗe ido
duk don ya tausashi zuciyarta.
Alhaji Maikuɗi ya shiga damuwa ƙwarai da gaske ganin
yadda uwar gidansa wato Binta ta shiga mummunan yanayi na damuwa da ɓacin rai
da baƙin ciki da yawan tunani. Yawan tunani yasa duk ta rame ta bushe ta
ƙanjame kamar ragowar yaƙi. Idanun ta duk sun kukkukkunbura luhu-luhu, sunyi ja
saboda yawan kuka sakamakon ɓacin ran baƙaƙen maganganun da ake yada mata wanda
suke mata turnuƙu a zuciyarta.
“Hajiya Binta,” Alhaji Maikuɗi yayi mata magana cikin
tattausan lafazi mai cike da tausayi. “Ki daina wannan yawan kukan da tunani da
kike yi. Wace iriyar baiwace Allah bai
miki ba. Baya ga kyan sura da Allah yayi miki ya kuma ni’imataki da hankali da tunani. Bugu da
ƙari, Allah bai barki haka ba sai ya
auraki ga mtum irina inda zaki ji daɗi ki huta. Baki da wata matsala saboda duk
abinda kika nema kina samu. Wace iriyar dukiyace ko wane irin jin daɗine bakya
samu anan gidan? Dan Allah ina so ki daina wannan yawan kukan. Ki barwa Allah
komai, ke ma idan kina da rabo sai Allah ya baki ɗa.”
Hajiya Binta ta yi aure tare da mai
gidanta Alhaji Maikuɗi kimanin shekara talatin da biyar da suka gabata. Amma
tsawon wannan lokaci bata taɓa samun haihuwaba. Ganin cewa Allah ya baiwa mai
gidanta tarin dukiya, sai Allah ya sa masa ƙaunar samun wanda zai gaje shi kuma
wanda zai ringa yi masa addu’a ko
bayan ba ransa. Duk da matsin lamba da Alhaji yake fuskanta daga wajen danginsa,
amma bai taɓa ɗaukar abinda suke faɗa masa yayi aiki da shi kai tsayi ba, ba tare
da yin shawara da Hajiya Binta ba. Hakan yasa suke ganin kamar ma ko ta shanye
shi ne. Kowa a dangin mijinta ya ɗau karan tsana ya ɗora mata saboda rashin
haihuwa. Abubuwa sukai ta ta’azzara,
dangantaka tai tsami tsakaninta da surukanta. Idan ta kawo musu abinci sai suki
karɓa, idan ta gaishesu sai su ƙi amsawa, sannan kuma yawan tsangwama ya hana
ta halartar duk wani irin taro a dangin, kamar suna, shan zabaina ko wuni. Kai
hatta wajen kamu ko buɗar kai sai da ya gagareta zuwa. Dalilinsu na wareta daga
cikinsu shi ne kada cuɗanya da ita yasa ƴaƴansu su shafi matsalar rashin
haihuwa irin tata. Sai dai kash! sun manta cewa Hajiya Binat ba juya bace domin
tsawon shekarun da tayi da mijinta basu tashi a banzaba. Ta sami ciki sau goma
sha tara illa dai kawai tanayin ɓarine. Da ba dan hakaba da tuni itama tana nan
tare da ƴaƴanta kamar kowa. Da tuni itama ta aurar kamar yadda ragowar
ƙawayenta suka aurar. Da tuni itama tana nan da babban ɗanta wanda da yana
raye, da ya sami gatan duniyannan daga mahifinsa. Wata biyu da aurensu ta sami
juna biyu, mai gidanta kuma yayi mata alƙawarin gida a Abuja da kano inda suke
zaune. Sannan yayi mata alƙawarin cewa zai mallaka mata kamfaninsa inda ake
sarrafa masa kayayyaki ita da jaririn da zata haifa masa. Amma hakan bai faruba
domin duk lokacin da ta sami ciki sai tayi ɓari. Duk waɗannan abubuwa na
kyautatawa da kaɓakin arziƙi bata same su ba, sai dai tana gani suka koma wajen kishiyoyinta
waɗanda suka zo bayan-bayanta amma suka haifawa Alhaji magada.
Rannan Hajiya Binta tana zaune a ɗaki ita
kaɗai sai ta ɗauko rediyo dan ta saurari wani shiri mai suna Hankalinka Gatanka daga gidan rediyo Gyara Kayanka inda ake gayyato masana daga fannonin rayuwa
daban-daban inda sukeyin bayani kan al’amura da suka shafi jama’a. Shi wanna shiri yana maida hankaline wajen
tattauna matsalolin da suka fi addabar al’umma kuma sukai ƙamari a cikin
zamantakewa. Hajiya Binta ta yi baƙuwa jiya, wadda ɗaya ce daga cikin ƙawayenta
tun na ƙuruciya wadda ta kawo mata ziyara. A lokacin ziyarar tatane suka
tattauna matsalolin da suka dami Hajiya Binta. Sai ƙawar tata ta bata shawara
akan ta ringa saurarar wannan shiri wataƙila ta gano menene matsalarta tunda
babban baƙon da za’a yi
hira da shi a wannan satin likita ne. Ai ko ta namma ta iya jin musabbabin abin
da ya jawo mata matsalar rashin haihuwa.
“Masu sauraro barkanmu da sake saduwa a
cikin wani sabon shirin na Hankalinka Gatanaka wanda ya saba zuwar muku daga
nan gidan rediyo Gyara Kayanka tare da ni Aishatu Sulaiman.” Hajiya Binta ta ƙara gyara zama ta ƙara
murɗo sautin rediyonta. “A tare
da ni a cikin shirin na yau muna tare da Dakta Yusha’u Garba babban likitan jama’a da kare cututtuka na sashen haihuwa da
cututtukan mata wato Abstetrics and
Gynocology, na babban asibitin ƙwararru na cikin gari. Yau a cikin shrin na
yau zamu tattauna da liktane akan matsaloli da illolin shaye-shayen miyagun
ƙwayoyi da kuma yin allurai barkatai ga lafiyar ƴaƴa mata, musamman ta fuskar hana su ɗaukar ciki da kuma
wani lokacin samun haihuwa.”
Hajiya ta ƙara zama sosai don taji za’a sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi.
“Likita a madadin masu sauraro filin
Hankalinka Gatanka na yi maka barka da zuwa.”Mai sanarwa tayi masa maraba.
“Jama’a salamu alaikum.” Shi ma yayi musu sallama.
“To kamar yadda na faɗa zamu tattauna da
likita tsawon sa’a ɗaya,
inda daga bisani zamu baku layukan waya da za ku samemu kai tsaye dan kuyi
tambaya ta hanayar bugo waya ko turo rubutaccen saƙo. Layukan da za’a iya samunmu su ne: 0706...80...77,”ƴar jaridar ta fadi lambar kuma ta shiga
cikin shirin gadan-gadan.
“Likita wai shin meye illar da shaye-shayen
ƙwayoyi da yin alluarai barkatai ke jawowa ga ƴaƴa mata musamman ɓangaren samun
ciki da kuma haihuwa?” ‘Ƴar jaridar ta tambaya.
“To da farko dai zan fara da tambayarki ta
farko wato illar shaye-shaye ga ƴaƴa mata ta fuskar samun ciki da kuma haihuwa.
Da farko dai abinda ake nufi da ƙwaya shi ne dukkan wani abu da za’a iya amfani da shi don a sha, ko a haɗiya,
ko a shaƙa, kuma dalilin haka ya jawo sauyin yanayi a jiki ta hanyar samar da
kuzari, ko kasala, ko samarda canjin tunani da juyawar hankali ko ƙwaƙwalwa.
“To abinda ake nufi da shan ƙwaya shi ne
amfani da ƙwayoyin da a likintance basu zama dole ba, ko a sha ba tare da
umarnin likitaba , ko a sha fiye da ƙima ko kuma shan ƙwayoyin da doka ta
haramta. A taƙaice dai akan iya cewa abin da ake nufi da shaye-shayen miyagun
ƙwayoyi shi ne yin amfani da magani dan wani dalili saɓanin aikinsa na asali.
Ko kuma yin amfani da haramtattun magunguna ko wanda ya saɓa da al’ada ko zamantakewa.
“To illar shaye-shaye ga mata yana da haɗarin
gaske saboda yakan iya hana su haifar yaro a raye abin da aka sani da ɓarin
ciki. Shi ɓarin ciki yana faruwane lokacin da ɗan tayi wato festus a turance, ya kai kimanin sati
ashirin a mahaifa. A bincike na baya-bayannan an gano cewa kimanin mata 6000 ne sukayi ɓari lokacin haihuwa a wata
shidan farko na shekarar da ta gabata wanda dukkaninsu bincike ya tabbatar da
cewa suna ta’ammali
da miyagun ƙwayoyi. Ana ɗaukar mabiyiya da kuma jini dan ayi gwajin sinadarin nicotine a jikin uwa. Shi wannnan
sinadari yana saka kuzari ko
watstsakarwa inda ake samunsa a cikin abubuwa kamar irin su cocaine. Akwai ragowar magunguna kamarsu
amphetamine
da sauran magunguna masu rage raɗadi kamar su morphine. Sauran su ne kamar su codein
da kuma tabar wi-wi da suransu. Sakamakon binciken ya nuna cewa yawan sinadarin
nicotine da yake a cikin jinin matan
ya zarta kaso 19 cikin ɗari yayinda wasu
kuma aka gano cewa suna ɗauke da wani adadi mai yawa na sinadarai masu sa
kasala wato stimulatns, wanda shi ma
dai yana da alaƙa da shaye-shaye ba bisa ƙa’ida ba. Amma hakan kuma ba yana nufin
cewa duk matan da sukeyin ɓariba suna ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.”
Hajiya Binta na zaune tana sauraron
rediyo, bata san lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta ba. Bayanda ta saurari
jawabin likita, sai ta ga ashe itace ta
jefa kanta cikin duk irin musifar da ta tsinci kanta a ciki ba. Tana kuka tana
cewa, “na
cuci kaina. Lokacin da ina buduruwa da bayan nayi aure nayi ta shan miyagun
ƙwayoyi wai ni ina ganin burgewace. Kaico na, yanzu gashi akan rashin haihuwa
ba irin wulaƙancin da ban gani ba.” Nan ta share hawayenta ta cigaba da
sauraren rediyo yayinda likita ya cigaba da bayani.
“To yanzu sai tambayarki ta biyu, wadda tayi
magana akan yin allurai ba bisa ƙa’ida ba. To kamar yadda aka sani itama
allura tana da illarta ga lafiyar kowa da kowa, musamman ga ƴaƴa mata a
matsyinsu na iyaye. Da farko dai idan akace allura ana nufin wata hanya ta zuba
ruwan sinadarin magani ga jiki ta hanyar yin amfani da allura da sirinji tare
da tsira alluarar a cikin jiki
gwargwadon zurfin da ya dace a cikin
fata. To a sakamakon yawan matsaloli da allura ke tattare da shi, hukumomin
lafiya na duniya suke umarni da a ringa amfani da magani na sha dan kaucewa
wadannan matsaloli.
“To tunda ya zamana cewa yawancin matasa
su suke amfani da alluarai ba bisa ƙa’ida ba ta jijiyoyin jini wato intravenous don su bugu. To kinga ke nan
yawan haɗarurrukan zasu fi afkuwa ga matasa kenan. Yawancin waɗannan allurai
sune allurar cocaine , pertozocine da kuma fortwine, wanda kowacce daga
cikinsu tana da illa ga jiki. Haɗarin abun ba wai kawai ya tsaya a bugarwa bane
kawai, babbar illar shi ne sinadaran da ke cikin irin waɗannan allurai kan iya
sanya mace yin ɓari. Bayan haka kuma suna zama hanyar yaɗa cututtukan jini a
tsakanin al’umma.
Misali ai kinga yaran suna da wani wuri inda suke zuwa akeyi musu allurar, wasu
kuma sukan sayi alluran su aje a gidanjensu. To amma duk da haka za ki ga ko waɗanda
suka aje alluran a gidajensu, za ki tarar cewa ba su kaɗai ne suke amfani da su
ba. Su kuma masu zuwa kanti dan ayi musu
alluarar, nan ma dai za ki tarar cewa akwai jam’a da yawa waɗanda ke zuwa don ayi musu
allurar , kuma mafi yawan lokaci da sirinji guda ɗaya. Tunda shi mai kantin kuɗi
kawai yake nema, kenan ko mutum nawa ne kawai zai iya yi musu alluara da
sirinji guda ɗaya. Shi dai indai buƙatarsa ta biya, ya amshe ƴan kuɗaɗensa shi
ke nan. To tsautsayi idan mai ɗauke da wata cuta irin HIV/AIDs ko kuma ciwon ƙoda wato Hepatitis B da C a turance yaje akayi masa alluara, sai wani ko
wata shi ma yaje akayi masa da wannan sirinjin da akayiwa mai ɗauke da waɗannan
cututtuka, to akwai haɗarin kamuwa da cuta. To kuma tunda su masuyin irin waɗannan
allurai basu da horo da ƙwarewar likitoci na ainihi, to zaki ga suna yin abin
ne ba tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace ba. Sakamakon haka, hukumar
lafiya ta duniya wato WHO ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna
cewa a cikin mutum miliyan 21 da suke kamuwa da ƙwayar cutar HIV/AIDS da
kuma ciwon hanta ko Hepatitis C,
kimanin mutum 260,00 ne suke kamuwa da cututtukan duk shekara ta sanadiyyar yin
amfani da alluarai da sirinjai marasa tsafta, ko yin allura ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma yiwa mutum fiye da ɗaya
alluara da sirinji guda ɗaya, ko kuma yin allura ba tare da wanke hannu ba, ko
ba tare da ansanya safa ba dan kariya, ko kuma yin amfani da sirinjin da ba’a rufeba da dai makamantan abubuwa shigen waɗanda muka lissafa.
“A ƙarshe Hajiya za ki ga cewa idan aka haɗa
duka, shaye-shayen da kuma alluaran, za ki ga cewa suna da illa ga lafiyar jiki
da ƙwaƙwalwa ta hanyar rage ƙarfin jiki da gurgunta ƙarfin garkuwar jiki abinda
aka fi sani a turance da antibody
mechanisms, da kuma jawo kansar hunhu, sannan kuma su jawo yawan yin fushi
wato depression.”
Da jin bayanin da likita yayi sai Hajiya
Binta ta fara zargin kanta tare da tabbatarwa da kanta cewa itama tana ɗauke da
waɗannan miyagun cututtuka. Nan ta ke ta faɗa kogin tunani inda ta tuna wasu
lokuta a baya da take tambayar mijinta zuwa asibiti amma sai ta zagaye ta tafi
kantin sayarda magani dan ayi mata allurar maye. Ba komai ya tayar mata da hankaliba
sai yadda ta tuna wani lokaci a baya yayinda abin ya ciyota, dole ta tashi ba
tare da umarnin mijinta ba ta fita don ayi mata alluara. Ko da ta isa kantin
magungunan sai ta tarar da layin mutane maza da mata kowa yana so ayi masa
allura. Amma maimakon suyi haƙuri a kawo sababbin sirinjai, sai kawai suka
ringa miƙa hannayensu anayi musu allurar da ƙwaya ɗayan sirinjin da ya rage.
Bayan da Alhaji ya dawo gida, sai ya isketa
a inda ta gama saurarar rediyo kwance male-male babu kuzari a jikinta kamar
gawa. Alhaji ya ɗauketa dan ya kaita asibiti dan ayi gwaji a gano abinda yake
damunta. Tun a baya Alhaji yayi ƙoƙarin kaita asibiti amma duk lokacin da ya
bujuro mata da maganar sai ta ɓata rai. Shi kuma sai ya ƙyaleta saboda baya san
ya ga ɓacin ranta. Da Alhaji ya gaji da irin wannan hali na ta, ga kuma cuta
taƙi ci taƙi cinyewa kullun sai rama take tana ƙarewa kamar kuɗin guzuri, dole
tasa ya ɗauketa ya kaita asibitin.
Bayan sun fito daga ɗakin gwajine sai
sakamakon bincike ya nuna cewa Hajiya Binta na ɗauke da ciwon sida AIDS , da kuma matsanancin ciwon hanta hepatitis C, da ciwon hunhu pulmonary
disease da anthrax,
da kuma ciwon ƙoda renal failure,
wanda dukkaninsu suna da alaƙane da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da alluran
maye. Bayan sun fito ne sai ta roƙi mai gidan nata da ya rufa mata asiri kada
ya bayyanawa ragowar kiyoshinta halin da take ciki, wanda nan take yayi mata
alƙawarin hakan.
Ganin cewa ba zai iya zama da mutumin da
yake ɗauke da irin waɗannan cututtukaba kashi-kashi dan gudun kada ragowar
iyalansa su kamu, sai ya saya mata gida a wata unguwa ta daban sannan ya cigaba
da ɗawainiya da ita ta fuskar abinci da magani har zuwa lokacin da ta tunkuyi
burji, wata biyu kacal bayan rabuwarsu. Amma duk da haka Alhaji bai furta mata
kalmar saki ba saboda tsabar ƙauna da yake mata, don har ta mutu tana nan a
matsayin matarsa ta aure inda yake fatan sake haɗuwarsu a aljanna a matsayin
mata da miji.